Bayanai sun nuna cewa, a cikin rubu'in farko na bana, yawan kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su da fitar da su ya karu da kashi 5 cikin 100, kana ana samun ci gaba da samun bunkasuwar cinikayyar waje a kai a kai, kana yawan shigo da kayayyaki da fitar da kayayyaki ya kai wani sabon matsayi. A halin da ake ciki na raguwar ci gaban kasuwancin duniya, irin wadannan nasarori ba su da sauki.